Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Kashegari kuma ya zauna a kan gadon shari'a, ya yi umarni a zo da Bulus. Da ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani a game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa.