Tun da yake duk abubuwan nan za a hallaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada, kuna sauraron ranar Allah, kuna gaggauta zuwanta! Da zuwanta kuwa za a kunna wa sammai wuta, su hallaka, dukkan abubuwa kuma da suke a cikinsu, wuta za ta narkar da su.