1
2Sar 2:9
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sa'ad da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka faɗa mini abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga wurinka.” Elisha ya ce, “Bari in sami rabo daga cikin ikonka domin in gaje ka.”
Compare
Explore 2Sar 2:9
2
2Sar 2:11
Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa.
Explore 2Sar 2:11
3
2Sar 2:10
Iliya kuwa ya ce, “Ka roƙi abu mai wuya, duk da haka, idan ka gan ni lokacin da za a ɗauke ni, to, abin da ka roƙa za ka samu, amma idan ba ka gan ni ba, to, ba za ka samu ba ke nan.”
Explore 2Sar 2:10
4
2Sar 2:14
Sai ya ɗauki alkyabban nan da ta faɗo daga wurin Iliya, ya bugi ruwan, yana cewa, “Ina Ubangiji, Allah na Iliya?” Sa'ad da ya bugi ruwan, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, Elisha kuwa ya haye.
Explore 2Sar 2:14
5
2Sar 2:12
Elisha kuwa ya gani, ya yi kuka yana cewa, “Ubana, ubana! Mai ikon tsaron Isra'ila! Ka tafi ke nan!” Bai kuwa ƙara ganin Iliya ba. Da baƙin ciki Elisha ya kama tufafinsa ya kece.
Explore 2Sar 2:12
6
2Sar 2:8
Sa'an nan Iliya ya tuɓe alkyabbarsa, ya naɗe ta, ya bugi ruwa da ita, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, dukansu biyu fa suka taka sandararriyar ƙasa suka haye.
Explore 2Sar 2:8
7
2Sar 2:1
Sa'ad da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa Sama cikin guguwa, Iliya da Elisha suka kama hanya daga Gilgal.
Explore 2Sar 2:1
Home
Bible
Plans
Videos