Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah, da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba mai yawan jinƙai, Allah na dukan ta'aziyya, shi da yake yi mana ta'aziyya a dukan wahalarmu, domin mu kuma mu iya ta'azantar da masu shan kowace irin wahala, da ta'aziyyar nan da mu ma muka samu a gun Allah.