“Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda Sarkin Assuriya, da dukan taron da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su. Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.