1
2Tar 20:15
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne.
Compare
Explore 2Tar 20:15
2
2Tar 20:17
Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”
Explore 2Tar 20:17
3
2Tar 20:12
Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”
Explore 2Tar 20:12
4
2Tar 20:21
Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce, “Ku yi godiya ga Ubangiji, Saboda madawwamiyar ƙaunarsa Tabbatacciya ce har abada.”
Explore 2Tar 20:21
5
2Tar 20:22
Sa'ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, 'yan kwanto, 'yan kwanton kuwa suka fatattake su.
Explore 2Tar 20:22
6
2Tar 20:3
Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.
Explore 2Tar 20:3
7
2Tar 20:9
‘Idan wani mugun abu ya same mu, kamar takobi, ko hukunci, ko annoba, ko yunwa, to, za mu tsaya a gaban wannan gida, a gabanka kuma, gama sunanka yana cikin gidan nan, idan mun yi maka kuka saboda wahalarmu, kai kuwa za ka ji, ka cece mu.’
Explore 2Tar 20:9
8
2Tar 20:16
Ku gangara ku fāɗa musu gobe. Ga shi kuwa, za su haura ta hawan Ziz, za ku tarar da su a ƙarshen kwarin a gabashin jejin Yeruyel.
Explore 2Tar 20:16
9
2Tar 20:4
Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji.
Explore 2Tar 20:4