1
1Tim 6:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.
Compare
Explore 1Tim 6:12
2
1Tim 6:10
Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.
Explore 1Tim 6:10
3
1Tim 6:6
Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.
Explore 1Tim 6:6
4
1Tim 6:7
Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.
Explore 1Tim 6:7
5
1Tim 6:17
Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.
Explore 1Tim 6:17
6
1Tim 6:9
Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha'awace-sha'awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.
Explore 1Tim 6:9
7
1Tim 6:18-19
Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri. Ta haka suke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don nan gaba, domin su riƙi rai wanda yake na hakika.
Explore 1Tim 6:18-19