Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka'idodina, sa'an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra'ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa'ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.