1
1Sar 19:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Bayan girgizar kuma, sai wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wutar. Bayan wutar sai ƙaramar murya.
Compare
Explore 1Sar 19:12
2
1Sar 19:4
Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
Explore 1Sar 19:4
3
1Sar 19:11
Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.
Explore 1Sar 19:11
4
1Sar 19:13
Sa'ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”
Explore 1Sar 19:13
5
1Sar 19:9
A can ya shiga wani kogo domin ya kwana. Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”
Explore 1Sar 19:9
6
1Sar 19:8
Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.
Explore 1Sar 19:8
7
1Sar 19:5
Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.”
Explore 1Sar 19:5
8
1Sar 19:7
Mala'ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.”
Explore 1Sar 19:7
9
1Sar 19:10
Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”
Explore 1Sar 19:10
10
1Sar 19:6
Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.
Explore 1Sar 19:6
11
1Sar 19:2
Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”
Explore 1Sar 19:2
12
1Sar 19:18
Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai (7,000) na Isra'ila waɗanda ba su rusuna wa Ba'al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”
Explore 1Sar 19:18
13
1Sar 19:19
Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa.
Explore 1Sar 19:19
14
1Sar 19:21
Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa'an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.
Explore 1Sar 19:21
15
1Sar 19:20
Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.” Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”
Explore 1Sar 19:20