1
Romawa 7:25
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
Compare
Explore Romawa 7:25
2
Romawa 7:18
Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.
Explore Romawa 7:18
3
Romawa 7:19
Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi.
Explore Romawa 7:19
4
Romawa 7:20
To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.
Explore Romawa 7:20
5
Romawa 7:21-22
Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah
Explore Romawa 7:21-22
6
Romawa 7:16
In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau.
Explore Romawa 7:16
Home
Bible
Plans
Videos