1
Romawa 4:20-21
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari.
Compare
Explore Romawa 4:20-21
2
Romawa 4:17
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.
Explore Romawa 4:17
3
Romawa 4:25
An miƙa shi ga mutuwa saboda zunubanmu, aka kuma tashe shi zuwa rai saboda Allah zai same mu marasa laifi.
Explore Romawa 4:25
4
Romawa 4:18
Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
Explore Romawa 4:18
5
Romawa 4:16
Saboda haka, alkawari yakan zo ta wurin bangaskiya ne, domin yă zama ta wurin alheri, don a tabbatar wa dukan zuriyar Ibrahim ba kawai ga waɗanda suke na doka ba amma har ma ga waɗanda suke na bangaskiyar Ibrahim. Shi ne kuwa mahaifinmu duka.
Explore Romawa 4:16
6
Romawa 4:7-8
“Masu albarka ne waɗanda aka gafarta laifofinsu, waɗanda aka kuma rufe zunubansu. Mai albarka ne mutumin da Ubangiji ba zai taɓa lissafta zunubansa ba.”
Explore Romawa 4:7-8
7
Romawa 4:3
Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
Explore Romawa 4:3
Home
Bible
Plans
Videos