1
Galatiyawa 4:6-7
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “ Abba, Uba.” Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
Compare
Explore Galatiyawa 4:6-7
2
Galatiyawa 4:4-5
Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.
Explore Galatiyawa 4:4-5
3
Galatiyawa 4:9
Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?
Explore Galatiyawa 4:9