L.Ƙid 35
35
Biranen Lawiyawa
1 #
Josh 21.1-42
A filayen Mowab a wajen Urdun daura da Yariko, Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce, 2“Ka umarci jama'ar Isra'ila, ka ce su ba Lawiyawa biranen da za su zauna a ciki daga cikin gādonsu, za su kuma ba Lawiyawa hurumi kewaye da biranen. 3Biranen za su zama nasu, inda za su zauna, hurumi kuwa domin shanunsu da sauran dukan dabbobinsu. 4Girman hurumin da za su ba Lawiyawa kewaye da biranen zai zama mai fāɗin kamu dubu kewaye da garun birnin. 5A bayan birnin za a auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen kudu, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu a wajen arewa. Wannan zai zama hurumin mutanen birnin. Birnin kuwa zai kasance a tsakiya. 6A cikin biranen da za a ba Lawiyawa, shida su zama na mafaka, inda za a yarda wa mai kisankai ya gudu zuwa can. Banda biranen mafaka guda shida, za a kuma ba su birane arba'in da biyu. 7Wato dukan biranen da za a ba Lawiyawa guda arba'in da takwas ne tare da huruminsu. 8Isra'ilawa za su ba Lawiyawa biranen nan bisa ga girman mallakarsu. Manyan kabilai za su ba su birane da yawa, amma ƙananan kabilai za su ba su birane kaɗan.”
Biranen Mafaka
(M.Sh 19.1-13; Josh 20.1-9)
9 #
M.Sh 19.2-4; Josh 20.1-9 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa, 10ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar Kan'ana, 11sai ku keɓe wa kanku biranen mafaka domin wanda ya yi kisankai da kuskure, ba da niyya ba, ya gudu zuwa can. 12Biranen za su zamar muku mafaka daga hannun mai bin hakkin jini, don kada a kashe mai kisankai tun bai riga ya tsaya a gaban shari'a ba. 13Sai ku zaɓi birane shida. 14Biranen mafaka uku a hayin gabashin Urdun, birane uku kuma a ƙasar Kan'ana. 15Waɗannan birane shida za su zama wuraren mafaka ga jama'ar Isra'ila, da baƙi, da baren da yake zaune tare da su, domin duk wanda ya kashe wani ba da niyya ba, ya tsere zuwa can.
16“Amma idan wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, ya yi kisankai, sai a kashe shi. 17Idan kuwa ya jefe shi da dutsen da ya isa a yi kisankai da shi, har ya mutu, ya yi kisankai ke nan, to, sai a kashe shi. 18Idan kuwa ya buge shi da makami na itace da ya isa a yi kisankai da shi, har kuwa ya mutu, ya yi kisankai ka nan, sai a kashe shi. 19Sai mai bin hakkin jinin ya kashe mai kisankan sa'ad da ya iske shi.
20“Idan saboda ƙiyayya ya laɓe, ya soke shi, ko ya jefe shi har ya mutu, 21ko kuma saboda ƙiyayya ya naushe shi da hannu har ya mutu, sai a kashe shi, gama ya yi kisankai ke nan. Wanda yake bin hakkin jinin, zai kashe wanda ya yi kisankai sa'ad da ya iske shi.
22“Amma idan bisa ga tsautsayi ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuwa idan ya jefe shi da kowane abu, ba a laɓe ba, 23ko ya jefe shi da dutsen da ya isa a kashe mutum da shi, ba da saninsa ba, shi kuwa ba maƙiyinsa ba ne, bai kuwa yi niyya ya cuce shi ba, amma ga shi kuwa, ya kashe shi, 24to, sai taron jama'a su hukunta tsakanin mai kisankan da mai bin hakkin jinin bisa ga waɗannan ka'idodi. 25Taron jama'a za su ceci mai kisankan daga hannun mai bin hakkin jinin. Su komar da shi a birnin mafaka inda ya je neman mafaka. Zai zauna can sai lokacin da babban firist da aka keɓe da tsattsarkan mai ya rasu. 26Amma idan a wani lokaci mai kisankan ya fita kan iyakar birnin mafaka inda yake, 27idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan iyakar birnin, ya kashe shi, bai yi laifi ba. 28Gama dole ne mai kisankan ya zauna cikin birnin mafaka inda yake, sai bayan rasuwar babban firist. Bayan rasuwar babban firist, mai kisankan yana iya komawa ƙasarsa.”
Ka'idodin Shaidu da Fansa
29“Waɗannan ka'idodi sun shafe ku da zuriyarku a duk inda kuke. 30#M.Sh 17.6; 19.15Duk wanda ya yi kisankai sai a kashe shi bisa ga shaidar shaidu, amma saboda shaidar mutum ɗaya ba za a kashe mutum ba. 31Kada ku karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, dole ne a kashe shi. 32Haka nan kuma kada ku karɓi fansa saboda wanda ya tsere zuwa birnin mafaka don ya koma ya zauna gidansa tun babban firist bai rasu ba. 33Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin. 34Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama'ar Isra'ila.”
@Bible Society of Nigeria 1979