L.Ƙid 34

34
Iyakokin Ƙasar
1Ubangiji ya ba Musa 2waɗannan umarnai domin jama'ar Isra'ila. Sa'ad da suka shiga ƙasar Kan'ana ga yadda iyakokin ƙasashensu za su zama. 3Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas. 4Sa'an nan kuma za ta nausa ta nufin hawan Akrabbim, ta ƙetare zuwa Zin, ta dangana da kudancin Kadesh-barneya, sa'an nan ta miƙa zuwa Hazar'addar, ta zarce ta bi ta Azemon. 5Iyakar za ta nausa daga Azemon zuwa rafin Masar, ta fāɗa bahar.
6Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma.
7Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor. 8Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad. 9Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.
10Iyakarsu a wajen gabas za ta tashi tun daga Haza-enan har zuwa Shefam. 11Sa'an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas. 12Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita.
13 # L.Ƙid 26.52-56 # Josh 14.1-5 Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Wannan ita ce ƙasar da za ku gāda ta hanyar jefa kuri'a. Ƙasar da Ubangiji ya umarta a ba kabilai tara da rabi. 14Gama kabilar Ra'ubainu da ta Gad da kuma rabin kabilar Manassa sun riga sun karɓi nasu gādo. 15Kabilan nan biyu da rabi sun karɓi nasu gādo a wancan hayin Urdun a gabashin Yariko.”
Shugabannin da za su Rarraba Kasa
16Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 17“Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun. 18Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar. 19Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza. 20Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu. 21Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu. 22Bukki ɗan Yogli daga kabilar Dan. 23Na wajen Yusufu, Haniyel ɗan Efod daga kabilar Manassa, 24da Kemuwel ɗan Shiftan daga kabilar Ifraimu. 25Elizafan ɗan Farnak daga kabilar Zabaluna. 26Faltiyel ɗan Azzan daga kabilar Issaka. 27Ahihud ɗan Shelomi daga kabilar Ashiru. 28Fedahel ɗan Ammihud daga kabilar Naftali.” 29Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba wa jama'ar Isra'ila gādon ƙasar Kan'ana.

目前选定:

L.Ƙid 34: HAU

高亮显示

分享

复制

None

想要在所有设备上保存你的高亮显示吗? 注册或登录