L.Ƙid 29

29
Hadayu na Idin Watan Bakwai
(L.Fir 23.23-25)
1A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni. 2Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin za su zama marasa lahani. 3Tare da dabbobin za a kuma miƙa hadaya ta lallausan gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimin, humushi biyu na garwa kuma tare da ragon. 4Za a miƙa humushin garwa na gāri tare da kowane ɗan rago. 5Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara. 6Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Hadaya a Ranar Kafara
(L.Fir 23.26-32)
7 # L.Fir 16.29-34 Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba. 8Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi ɗaya, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani. 9Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da ragon, 10da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago. 11Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, banda hadaya don zunubi saboda yin kafara, da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha.
Hadayu na Idin Bukkoki
(L.Fir 23.33-44)
12 # L.Fir 23.34; M.Sh 16.13-15 A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai. 13Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da 'yan bijimai goma sha uku, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani. 14Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta lallausan gāri wanda aka kwaɓa da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da kowane rago, 15da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago. 16Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
17A rana ta biyu ta idin za a miƙa bijimai goma sha biyu, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dukan dabbobin su zama marasa lahani. 18Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 19Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gari, da hadayarsu ta sha.
20A rana ta uku ta idin za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 21Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 22Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
23A rana ta huɗu ta idin za a miƙa bijimai goma, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 24Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 25Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
26A rana ta biyar ta idin za a miƙa bijimai tara, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 27Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 28Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
29A rana ta shida ta idin za a miƙa bijimai takwas, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 30Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 31Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya taƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
32A rana ta bakwai ta idin za a miƙa bijimai bakwai, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani. 33Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 34Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
35A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba. 36Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi, da rago, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin su zama marasa lahani. 37Za a miƙa hadaya ta gāri da hadaya ta sha tare da bijimin, da ragon, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar. 38Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
39Waɗannan su ne hadayun da za a miƙa wa Ubangiji a lokacin idodinsu, duk da hadayunsu na wa'adi, da na yardar rai, da na ƙonawa, da na gāri, da na sha, da na salama.
40Musa kuwa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila kome da kome kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

目前选定:

L.Ƙid 29: HAU

高亮显示

分享

复制

None

想要在所有设备上保存你的高亮显示吗? 注册或登录