L.Ƙid 28
28
Hadaya na Kullum
(Fit 29.38-46)
1Sai Ubangiji ya umarce Musa, 2ya dokaci Isra'ilawa su tabbatar cewa sun miƙa wa Allah hadaya ta abinci tare da hadayun da za a yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci bisa ga yadda ake bukata.
3Waɗannan su ne hadayu na abinci da za a miƙa wa Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, raguna biyu 'yan bana ɗaya ɗaya marasa lahani. 4A miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice, 5da kuma mudun lallausan gari, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu'in moɗa. 6Hadaya ce ta ƙonawa kullum, wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji. 7Hadaya ta sha za ta zama rubu'in moɗa na ruwan inabi domin kowane ɗan rago. Za a kwarara hadaya ta sha mai gafi ga Ubangiji a bagade. 8Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice, tare da hadaya ta gari kamar ta safe, da hadayarsa ta sha. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Hadayu na Ranar Asabar
9A rana Asabar kuwa za a miƙa 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da mudu biyu na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai, domin yin hadaya ta gari tare da hadayarsa ta sha. 10Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha.
Hadayu na Ɗaya ga Wata
11A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma 'yan raguna bakwai bana daya daya; marasa lahani, 12hadaya ta gari kuma, a kwaɓa gari humushi uku na garwa da man zaitun don kowane bijimi, da gari humushi biyu na garwa don rago, 13da kuma gari humushin garwa don ɗan rago. Waɗannan su ne hadayu na abinci na ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 14Hadaya ta sha kuwa za ta zama rabin moɗa na ruwan inabi don kowane bijimi, sulusin moɗa kuma don kowane rago, rubu'in moɗa don kowane ɗan rago. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane wata na shekara. 15A kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi ga Ubangiji tare da hadaya ta ƙonawa, da hadayarta ta sha.
Hadayu na Idin Abinci Marar Yisti
(L.Fir 23.5-8)
16 #
Fit 12.1-13; M.Sh 16.1,2 Za a yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga watan fari. 17#Fit 12.14-20; 23.15; 34.18; M.Sh 16.3-8Kashegari kuwa za a fara idin kwana bakwai. A kwanakin nan, sai a riƙa cin abinci marar yisti. 18Za ku yi tsarkakakken taro a ranar fari ta idin, ba za a yi aiki ba. 19Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya ga Ubangiji. Dukansu su zama marasa lahani. 20Za a kuma miƙa hadaya ta gari tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da man zaitun, gari humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gari humushi biyu tare da kowane rago, 21gari humushi ɗaya tare da kowane ɗan rago. 22Za a miƙa bunsuru guda don yin hadaya don zunubi, domin yin kafara. 23Za a miƙa waɗannan hadayu banda hadaya ta ƙonawa wadda akan miƙa kowace safiya. 24Haka za a miƙa abinci na hadaya ta ƙonawa kowace rana har kwana bakwai, domin daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Za a kuma riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta sha. 25A rana ta bakwai za a yi tsattsarkan taro, ba za a yi aiki ba.
Hadayun Idin Girbi
(L.Fir 23.15-22)
26 #
Fit 23.16; 34.22; M.Sh 16.9-12 Za a yi tsattsarkan taro a ranar nunan fari, wato idi na mako bakwai lokacin da za a miƙa wa Ubangiji hadaya da sabon hatsi. A ranar ba za a yi aiki ba. 27Za a miƙa hadaya ta ƙonawa, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. 28Za a miƙa hadaya ta gāri tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da mai, gari humushi uku na garwa, za a miƙa tare da kowane bijimi, humushi biyu na garwa don rago, 29da humushin garwa don kowane ɗan rago. 30Za a miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi, domin a yi kafara. 31Banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, sai a miƙa waɗannan tare da hadayarsu ta sha. Dabbobin su zama marasa lahani.
@Bible Society of Nigeria 1979