1
Mar 5:34
Littafi Mai Tsarki
HAU
Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”
Сравнить
Изучить Mar 5:34
2
Mar 5:25-26
Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi.
Изучить Mar 5:25-26
3
Mar 5:29
Nan take zubar jininta ta tsaya, ta kuma ji a jikinta an warkar da cutarta.
Изучить Mar 5:29
4
Mar 5:41
Ya kama hannunta, ya ce mata, “Talita ƙumi”, wato, “Ke yarinya, ina ce miki, tashi.”
Изучить Mar 5:41
5
Mar 5:35-36
Yana cikin magana, sai ga waɗansu daga gidan shugaban majami'a suka ce, “Ai, 'yarka ta rasu, me kuma za ka wahalar da Malamin?” Amma Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, ya ce wa shugaban majami'a, “kada ka ji tsoro, ka ba da gaskiya kawai.”
Изучить Mar 5:35-36
6
Mar 5:8-9
Ya faɗi haka ne domin Yesu ya ce masa, “Rabu da mutumin nan, kai wannan baƙin aljan!” Yesu ya tambaye shi, “Me sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli, don muna da yawa.”
Изучить Mar 5:8-9