1
Mar 2:17
Littafi Mai Tsarki
HAU
Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”
Сравнить
Изучить Mar 2:17
2
Mar 2:5
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.”
Изучить Mar 2:5
3
Mar 2:27
Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba.
Изучить Mar 2:27
4
Mar 2:4
Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayye yake kwance a kai.
Изучить Mar 2:4
5
Mar 2:10-11
Amma don ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya” sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”
Изучить Mar 2:10-11
6
Mar 2:9
Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya’?
Изучить Mar 2:9
7
Mar 2:12
Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”
Изучить Mar 2:12