1
Yah 19:30
Littafi Mai Tsarki
HAU
Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.
Сравнить
Изучить Yah 19:30
2
Yah 19:28
Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”
Изучить Yah 19:28
3
Yah 19:26-27
Da Yesu ya ga uwa tasa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa uwa tasa, “Iya, ga ɗanki nan!” Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Изучить Yah 19:26-27
4
Yah 19:33-34
Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano.
Изучить Yah 19:33-34
5
Yah 19:36-37
Wannan kuwa don a cika Nassi ne cewa, “Ƙashinsa ɗaya ba za a karya ba.” Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
Изучить Yah 19:36-37
6
Yah 19:17
Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota.
Изучить Yah 19:17
7
Yah 19:2
Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura.
Изучить Yah 19:2