1Kor 2
2
Shelar Almasihu Gicciyeyye
1Sa'ad da na zo wurinku, 'yan'uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta wurin iya magana ko gwada hikima ba. 2Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye. 3#A.M 18.9 Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai. 4Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu, 5kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.
Bayani daga Ruhun Allah
6Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba. 7Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu. 8A cikin masu mulkin zamanin nan, ba wanda ya gane hikimar nan, don da sun gane ta, da ba su gicciye Ubangiji Maɗaukaki ba. 9#Ish 64.4 Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa,
“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba,
Kunne bai taɓa ji ba,
Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba,
Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”
10mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah. 11Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake. 13Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al'amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.
14Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su. 15Mutumin da yake na ruhu kuwa yakan rarrabe da kome, shi kansa kuma ba mai jarraba shi. 16#Ish 40.13 “Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.
Nu geselecteerd:
1Kor 2: HAU
Markering
Kopiëren
Vergelijk
Delen
Wil je jouw markerkingen op al je apparaten opslaan? Meld je aan of log in
@Bible Society of Nigeria 1979