1Kor 1
1
Gaisuwa
1Daga Bulus, manzo kirayayye na Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Sastanisu, 2#A.M 18.1 zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.
3Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Godiya saboda Bayebaye na Ruhu
4Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu, 5har ta kowace hanya aka wadata ku a cikinsa, a wajen yin magana duka da ilimi duka, 6domin kuwa an tabbatar da shaida a kan Almasihu a cikinku. 7Har ma ku ba kāsassu ba ne a wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 8wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijinmu.
Tsattsaguwa a Ikkilisiya
10Na roƙe ku 'yan'uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra'ayinku ɗaya. 11Don kuwa, ya 'yan'uwana, mutanen gidan Kuluwi sun ba ni labari, cewa akwai jayayya a tsakaninku. 12#A.M 18.24 Abin da nake nufi, shi ne kowannenku yana faɗar abu dabam, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afolos ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “ni na Almasihu ne.” 13Ashe, Almasihu a rarrabe yake? Ko Bulus ne aka gicciye dominku? Ko kuwa an yi muku baftisma ne da sunan Bulus? 14#A.M 18.8; A.M 19.29; Rom 16.23 Na gode Allah da ban yi wa waninku baftisma ba, banda Kirisbus da Gayus, 15kada wani ya ce da sunana ne aka yi muku baftisma. 16#1Kor 16.15 Ai, kuwa lalle na yi wa jama'ar gidan Istifanas ma. Amma banda waɗannan ban san ko na yi wa wani baftisma ba.
17Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.
Almasihu Ikon Allah Ne, da Hikimarsa
18Maganar gicciye, maganar wauta ce ga waɗanda suke hallaka, amma ƙarfin Allah ce a gare mu, mu da ake ceto. 19#Ish 29.14 Domin a rubuce yake cewa,
“Zan rushe hikimar mai hikima,
Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”
20 #
Ayu 12.17; Ish 19.12; 33.18;
Ish 44.25
To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba? 21Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara. 22Yahudawa kam, mu'ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suka nema su samu, 23mu kuwa muna wa'azin Almasihu gicciyeyye, abin sa yin tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga al'ummai, 24amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al'ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah. 25Domin abin da aka zata wauta ce ta Allah, ya fi hikimar ɗan adam, abin da kuma aka zata rauni ne na Allah, ya fi duk ƙarfin ɗan adam.
26Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku 'yan'uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa. 27Amma Allah ya zaɓi abin da yake wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da yake rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa. 28Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin yă shafe abubuwan da suke akwai. 29Wannan kuwa duk don kada wani ɗan adam yă yi fariya a gaban Allah ne. 30Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa. 31#Irm 9.24 Saboda haka, “Duk mai yin alfarma, yă yi da Ubangiji” (abin da yake a rubuce ke nan).
Nu geselecteerd:
1Kor 1: HAU
Markering
Kopiëren
Vergelijk
Delen
Wil je jouw markerkingen op al je apparaten opslaan? Meld je aan of log in
@Bible Society of Nigeria 1979