1
Mat 15:18-19
Littafi Mai Tsarki
HAU
Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum. Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke.
Vergelijk
Ontdek Mat 15:18-19
2
Mat 15:11
Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”
Ontdek Mat 15:11
3
Mat 15:8-9
“ ‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni. A banza suke bauta mini, Don ka'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’ ”
Ontdek Mat 15:8-9
4
Mat 15:28
Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.
Ontdek Mat 15:28
5
Mat 15:25-27
Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!” Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.” Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”
Ontdek Mat 15:25-27