Duk wannan kuwa yin Allah ne, shi da ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu aikin shelar sulhuntawar, wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta 'yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa.