Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi. Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.