योजना की जानकारी

अनुग्रह का गाननमूना

अनुग्रह का गान

दिन 4 का 5

Kuna jin su kowace rana ... muryoyi. Wasu suna cikin kanku. Wasu suna kan labarin zamantakewar ku. Wasu sun fito daga abokanku. Wasu suna fitowa ne daga waɗanda suke ƙinku a fili.

Su ne muryoyin da ke ƙoƙarin gaya muku ko ku wanene... da abin da zai sa ku zama wanɗanda ya kamata ku zama.

Matsala ɗaya da duk waɗannan muryoyin ita ce ba za su iya cika alƙawarinsu ba. Shaidar ku ba abu ne da sai kun samu ba, gano da kanku, ko ku yi yaƙi don kiyayewa. Kyauta ce daga Uangiji.

Fasto da masanin tauhidi John Piper sun rubuta, "Dangani da Yesu, ba za mu rasa kanmu na gaskiya ba, amma za mu zama kanmu na gaskiya, kaɗai a wajensa."

To ina ne kuke gano kanku na gaskiya?

A cikin kudi? A cikin mabiya? A cikin nasara? A cikin kamanni? A siyasa? A cikin mulki? A cikin hali? A cikin jima'i?

A'a, a wajen Yesu kadai.

Corinthians ta biyu 5:17 ta ce, “Saboda haka, idan kowa yana tare da Almasihu, sabuwar halitta ta zo: tsohuwar ta riga ta wuce, sabuwar tana nan!” (NIV)

Wannan babban labari ne! Yana nufin ku waye ba abin da za a yi muhawara ba ne. Shaidar ku waye zai zo ne daga wajen Ubangijin da ya halicce ku. Ya ce, “Ku sabuwar halitta ce kar saboda Yesu... kuna da ƴanci ba sai kun yi ƙoƙarin neman yardar wasu ba, kuna da ƴanci ba sai kun yi ƙoƙarin nuna darajar ku ba, ba sai kun guje wa abubuwan da suka gabata ba.”

Cikin alherin Yesu, ba ku zama abin da kuka kasance ba, abin da wasu suke tsammani a kanku, ko abin da duniya ta ce ya kamata ku zama. Maimakon haka, kai ƙaunataccen ɗan Ubangiji ne.

Kuma a nan ne ainihin abu me kyau yake...

Domin Ubangiji ne ya halicce ku, gwargwadon kusancin ku da shi, gwargwadon yadda za ku kai matuƙa wajen zama yadda Ya halicce ku. Ta wata hanya, Ubangiji zai mayar da kuke na asali, abin da duk muke kashe lokaci da ƙoƙari don mu gano da kanmu.

Kun gane abin da hakan yake nufi?

A duk lokacin da wasu suka ɓata ku, sai ku tambayi kanku, ko kuma ku ji motsin neman yardar duniya, kuna da gaskiyar da za ku riƙe. Kuna iya tsayuwa tsayin daka ku ce, “Na san ko ni wane ne. Ba ya cikin tambaya. Ni ɗan Ubangiji ne, an gafarta mini, an ƴanta ni, kuma na samu sabo ta hanyar Yesu.”

Ci gaba, gwada shi a yau; a wurin aiki, a zamatakewa, tare da abokanku, kawai a cikin zuciyarku. Tabbatar da wanda Ubangiji ya ce kai shi ne ta hanyar Yesu. Karɓe shi. Ku yarda da shi. Rayu a ciki. Kuma kada ku manta yadda Ubangiji yake son ku.

Albarka,

—Nick Hall

पवित्र शास्त्र

दिन 3दिन 5

इस योजना के बारें में

अनुग्रह का गान

विवरण इस भक्तिमय अनुग्रह गान के माध्यम से आपके प्रति ईश्वर के प्रेम की गहराई का पता लगाएं। इंजीलवादी निक हॉल आपको 5-दिवसीय शक्तिशाली भक्ति के माध्यम से मार्गदर्शन करेगा जो आपको आपके ऊपर गाए गए ईश्वर की कृपा के गान में श...

More

हम यह योजना प्रदान करने के लिए PULSE Outreach को धन्यवाद देना चाहते हैं। और अधिक जानकारी के लिए कृपया विजिट करें: https://anthemofgrace.com/

YouVersion आपके अनुभव को वैयक्तिकृत करने के लिए कुकीज़ का उपयोग करता है। हमारी वेबसाइट का उपयोग करके, आप हमारी गोपनीयता नीति में वर्णित कुकीज़ के हमारे उपयोग को स्वीकार करते हैं।