योजना की जानकारी

अनुग्रह का गाननमूना

अनुग्रह का गान

दिन 2 का 5

Abin da na fi so game da bin Yesu kuma shi ne mafi ƙarancin abin da na fi so game da bin Yesu.

Bara in yi bayani…

Na ji daɗin gayyatar da ubangiji Ya yi min cikin iyalinsa. Ban cancanci komai daga ciki ba. Abin da na cancanta kawai shi ne hukuncin zunuban rayuwata, kuma babu abin da zan iya yi don gyara shi. Sai ya zama kamar ba zan iya shiga kulob ɗin ba... kuɗin kofar ya yi yawa… sannan sai Ubangiji ya shigo ya biya min kuɗin hanya.

Alheri kenan.

Amma a nan ne abin yake… Alherin Ubangiji na kowa da kowa ne, har da mutanen da suke wahalar da rayuwar ku.

Dukkanmu muna da mutane a rayuwarmu waɗanda suke kai mu ƙasa, suna tura mu hanyar da ba ta dace ba, kuma gabaɗaya kawai suna haukatar da mu. Wataƙila wani ne da ka sani kai da shi. Ko wataƙila wani ne akan yanar gizo-gizo.

Sau da yawa a duniyarmu ta yau, mutanen da suka fi damunmu su ne waɗanda ba mu taɓa haɗuwa da su ba; jigon jama'a, jam'iyyar siyasa, mai tasiri akan TikTok.

Ko wanene ma, abin da ya fi zama gama gari shi ne idan wani ya ɓata mana rai, sai su zama “su”.

Kamar, ba za ku iya yin tunani irin nasu ba. Ba za ku iya magana da su ba. Ba za ku iya girmama su ba. Ba za ku iya son su ba.

Ƴan Adam suna da gwanintar laƙabi da aibata mutane – galibi duka gungun mutane – ta amfani da mizanin da ba za mu taɓa yin amfani da shi don hukunta kanmu ba. Na yi. Ina fata ku ma kun yi.

Ku yabi Ubangiji da bai yi ba!

Domin abu game da alheri shi ne cewa dukkan mu muna buƙatar shi. Kuma da samun shi, Ubangiji ya kira ku da ni don miƙa alherinsa mai ban mamaki ga wasu.

Colossians 3:13 ta ce,

“Ku yi haƙuri da juna, ku gafarta wa juna idan ɗayanku yana jin haushin wani. Ka gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maka.”

Ba na bin Ubangiji bashin soyayyarsa. Ba na binsa bashin gafara. Ba na binsa bashin dangantaka da shi ko alƙawarin rayuwa ta har abada a aljanna. Duk wannan tsantsar alheri ne kawai. Don haka, tambayar da ta zama dole mu yi wa kanmu ita ce: ta yaya za mu sami irin wannan alheri mai ban mamaki daga wurin Ubangiji ba tare da mun miƙa ta ga wasu ba?

Alheri ba yana nufin ka yarda da duk abin da wani ya faɗa ko ya yi ba. Alheri ba yana nufin ka bar zunubi a duniya ba. Alheri ba yana nufin ba ku tsaya kan abin da yake daidai ba.

Alheri yana nufin ba ka aibata wani ko ka riƙe ƙaunarka saboda sun yi maka laifi ko ma sun yi wani abu ba daidai ba. Me ya sa?

Domin haka Ubangiji yake son ku… kuma haka Ubangiji yake ƙaunar su.

Albarka,

—Nick Hall

पवित्र शास्त्र

दिन 1दिन 3

इस योजना के बारें में

अनुग्रह का गान

विवरण इस भक्तिमय अनुग्रह गान के माध्यम से आपके प्रति ईश्वर के प्रेम की गहराई का पता लगाएं। इंजीलवादी निक हॉल आपको 5-दिवसीय शक्तिशाली भक्ति के माध्यम से मार्गदर्शन करेगा जो आपको आपके ऊपर गाए गए ईश्वर की कृपा के गान में श...

More

हम यह योजना प्रदान करने के लिए PULSE Outreach को धन्यवाद देना चाहते हैं। और अधिक जानकारी के लिए कृपया विजिट करें: https://anthemofgrace.com/

YouVersion आपके अनुभव को वैयक्तिकृत करने के लिए कुकीज़ का उपयोग करता है। हमारी वेबसाइट का उपयोग करके, आप हमारी गोपनीयता नीति में वर्णित कुकीज़ के हमारे उपयोग को स्वीकार करते हैं।