YouVersion Logo
Search Icon

Luk 4

4
Shaiɗan Ya Gwada Yesu
(Mat 4.1-11; Mar 1.12-13)
1Yesu kuma cike da Ruhu Mai Tsarki sai ya dawo daga Kogin Urdun. Ruhu na iza shi zuwa jeji, 2har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa. 3Iblis ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama gurasa,” 4#M.Sh 8.3 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.’ ” 5Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido. 6Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama. 7In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.” 8#M.Sh 6.13 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa,
“ ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada,
Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”
9Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan, 10#Zab 91.11,12don a rubuce yake cewa,
“ ‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’
11da kuma
‘Za su tallafe ka,
Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”
12 # M.Sh 6.16 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ” 13Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.
Yesu Ya Fara Hidima a Galili
(Mat 4.12-17; Mar 1.14-15)
14Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen. 15Ya yi ta koyarwa a majami'unsu, duk ana girmama shi.
An Ƙi Yesu a Nazarat
(Mat 13.53-58; Mar 6.1-6)
16Ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami'a a ran Asabar kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe domin ya yi karatu. 17Aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta cewa,
18 # Ish 61.1,2 “Ruhun Ubangiji yana tare da ni,
Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara.
Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru,
In kuma buɗe wa makafi ido,
In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,
19In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.”
20Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami'a suka zuba masa ido. 21Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.” 22Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?” 23Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ” 24#Yah 4.44 Ya ce kuma, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da yake yardajje a garinsu. 25#1Sar 17.1 Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar. 26#1Sar 17.8-16 Duk da haka ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata mace kaɗai a Zarifat ta ƙasar Sidon wadda mijinta ya mutu. 27#2Sar 5.1-14 A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra'ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na'aman, mutumin Suriya, kaɗai.”
28Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami'a suka husata ƙwarai. 29Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa. 30Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.
Mai Baƙin Aljan
(Mar 1.21-28)
31Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar. 32#Mat 7.28,29 Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take. 33A majami'ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce, 34“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.” 35Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba. 36Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.” 37Labarinsa duk ya bazu ko'ina a kewayen ƙasar.
Yesu Ya Warkar da Surukar Bitrus
(Mat 8.14-15; Mar 1.29-31)
38Sai ya tashi daga majami'a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita. 39Sai ya tsaya a kanta, ya tsawata wa zazzaɓin, ya kuwa sake ta. Nan take ta tashi ta yi musu hidima.
Yesu Ya Warkar da Mutane da yawa da Maraice
(Mat 8.16-17; Mar 1.32-34)
40A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su. 41Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.
Yesu Ya Tafi Yin Wa'azi
(Mar 1.35-39)
42Da gari ya waye ya fita, ya tafi wani wurin inda ba kowa. Sai taro masu yawa suka yi ta nemansa, suka je wurinsa. Sonsu ne su tsaishe shi, don kada ya tashi daga gare su, 43amma ya ce musu, “Lalle ne in yi wa sauran garuruwa bisharar Mulkin Allah, domin saboda wannan nufi ne aka aiko ni.” 44Sai ya yi ta yin wa'azi a majami'un ƙasar Galili.

Currently Selected:

Luk 4: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy