YouVersion Logo
Search Icon

Waƙar Waƙoƙi 1

1
1Waƙar Waƙoƙin Solomon.
Ƙaunatacciya#1.2 Da farko dai an nuna masu magana ko namiji ko ta mace bisa ga jinsi na wakilan sunayen da Ibraniyanci suka yi amfani da su, a gefen shafi ta wurin salon Ƙaunatacce da Ƙaunatacciya daki-daki. An nuna sauran kalmomin da Abokai. A waɗansu wurare akwai shakka game da ɓangarori da salo.
2Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa,
gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3Ƙanshin turarenka mai daɗi ne;
sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne.
Shi ya sa mata suke ƙaunarka!
4Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri!
Bari sarki yă kai ni gidansa.
Ƙawaye
Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai,
za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi.
Ƙaunatacciya
Daidai ne su girmama ka!
5Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa.
Ya ku ’yan matan Urushalima,
ni baƙa ce kamar tentunan Kedar,
kamar labulen tentin Solomon.#1.5 Ko kuwa Salma
6Kada ku harare ni domin ni baƙa ce,
gama rana ta dafa ni na yi baƙa.
’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni
suka sa ni aiki a gonakin inabi;
na ƙyale gonar inabi na kaina.
7Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka
kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana.
Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe
kusa da garkunan abokanka?
Ƙawaye
8Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba,
to, ki dai bi labin da tumaki suke bi
ki yi kiwon ’yan awakinki
kusa da tentunan makiyaya.
Ƙaunatacce
9Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya
mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.
10’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau,
wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.
11Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya,
da adon azurfa.
Ƙaunatacciya
12Yayinda sarki yake a teburinsa,
turarena ya bazu da ƙanshi.
13Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni,
kwance a tsakanin ƙirjina.
14Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni
daga gonakin inabin En Gedi.
Ƙaunatacce
15Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata!
Kai, ke kyakkyawa ce!
Idanunki kamar na kurciya ne.
Ƙaunatacciya
16Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena!
Kai, kana ɗaukan hankali!
Gadonmu koriyar ciyawa ce.
Ƙaunatacce
17Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu;
fir su ne katakan rufin gidanmu.

Currently Selected:

Waƙar Waƙoƙi 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy