YouVersion Logo
Search Icon

Rut 1

1
Na’omi ta rasa mijinta da ’ya’yanta maza
1A kwanakin da mahukunta suke mulki#1.1 A gargajiyance alƙalai an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab. 2Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can.
3To, Elimelek mijin Na’omi ya rasu, aka bar ta da ’ya’yanta maza biyu. 4Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma, 5sai Malon da Kiliyon suka mutu su ma, aka kuma bar Na’omi babu ’ya’yanta maza biyu da kuma mijinta.
Na’omi da Rut sun dawo Betlehem
6Sa’ad da ta ji a Mowab cewa Ubangiji ya zo don yă taimaki mutanensa ta wurin tanada musu da abinci, sai Na’omi tare da surukanta suka shirya su koma gida daga can. 7Tare da surukanta biyu suka bar inda suka zauna suka kuma kama hanya da za tă komar da su zuwa ƙasar Yahuda.
8Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, “Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji yă nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni. 9Bari Ubangiji yă sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji.”
Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi 10suka ce mata, “Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki.”
11Amma Na’omi ta ce, “Ku koma gida, ’ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ’ya’ya maza da za su zama mazanku ne? 12Ku koma gida ’ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ’ya’ya maza, 13za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ’ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!”
14A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.
15Sai Na’omi ta ce, “Duba, ’yar’uwanki ta koma zuwa ga mutanenta da kuma allolinta. Ki koma tare da ita.”
16Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. 17Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.” 18Sa’ad da Na’omi ta gane cewa Rut ta ƙudura tă tafi tare da ita, sai ta daina nema tă koma.
19Saboda haka matan biyu suka ci gaba da tafiya sai da suka isa Betlehem. Da suka isa Betlehem, sai dukan garin ya ruɗe saboda su, matan kuwa suka ce, “Na’omi ce wannan kuwa?”
20Ta ce musu, “Kada ku kira ni Na’omi.#1.20 Na’omi yana nufin mai daɗi; haka ma a aya 21. Ku kira ni Mara#1.20 Mara yana nufin ɗaci. gama Maɗaukaki#1.20 Da Ibraniyanci an rubuta Shaddai ne a nan. ya sa raina ya yi ɗaci sosai. 21In tafi cikakke, amma Ubangiji ya dawo da ni ba kome. Don me kuke kirana Na’omi? Ubangiji ya wahalshe#1.21 Ko kuwa ba da shaida gāba da ni. ni, Maɗaukaki ya kawo mini masifa.”
22Na’omi fa ta koma daga Mowab tare da Rut mutuniyar Mowab, surukarta, suka kai Betlehem a lokacin da ake fara girbin sha’ir.

Currently Selected:

Rut 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy