YouVersion Logo
Search Icon

Zabura 1

1
LITTAFI NA ƊAYA
Zabura 1–41
Zabura 1
1Mai farin ciki ne mutumin
da ba ya aiki da shawarar mugaye
ko yă yi abin da masu zunubi suke yi
ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,
kuma yana ta nazarinta dare da rana.
3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,
wanda yake ba da amfani a daidai lokaci
wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.
Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
4Ba haka yake da mugaye ba!
Su kamar yayi ne
da iska take kwashewa.
5Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,
balle a sami masu zunubi a taron adalai.
6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,
amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

Currently Selected:

Zabura 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy