YouVersion Logo
Search Icon

Karin Magana 1

1
Gabatarwa, manufa da kuma kan magana
1Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
2Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;
don ganewa kalmomi masu zurfi;
3don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,
kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
4don sa marar azanci yă yi hankali,
yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
5bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,
bari masu tunani kuma su sami jagora,
6don su fahimci karin magana da kuma misalai,
kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
7Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye#1.7 Kalmomin Ibraniyancin da aka rubuta wawa a cikin Littafi Karin Magana, da kuma ko’ina a cikin Tsohon Alkawari sau da yawa, yana nufin wani wanda ya rasa cikakken ɗa’a ne. sun rena hikima da horo.
Gargaɗi don a rungumi hikima
Jan kunne game da jaraba
8Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
9Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
10Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka,
kada ka yarda.
11In suka ce, “Zo mu tafi;
mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe,
mu fāɗa wa marasa laifi;
12mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari,
kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
13za mu sami dukiya masu daraja iri-iri,
mu kuma cika gidajenmu da ganima;
14ka haɗa kai da mu,
za mu kuwa raba abin da muka sato”
15ɗana, kada ka tafi tare da su,
kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
16gama ƙafafunsu kan yi sauri ga yin zunubi,
suna saurin yin kisankai.
17Ba shi da amfani a kafa tarko
a idanun dukan tsuntsaye!
18Waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko;
ba sa kama kome, sai rayukansu!
19Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau;
ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.
Jan kunne game da ƙin hikima
20Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,
tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,#1.21 Da Ibraniyanci; Seftuwajin / a bisa katanga
tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22“Har yaushe ku da kuke marasa azanci#1.22 Kalmar Ibraniyancin da aka rubuta marar azanci a cikin Littafin Kari Magana gaba ɗaya tana nufin marar ɗa’a da kuma wanda yana aikata mugunta ne. za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?
Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku
wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23Da a ce kun saurari tsawatata,
da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata
in kuma sanar da ku tunanina.
24Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira
ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25da yake kun ƙi dukan shawarata
ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku,
zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
27sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri,
sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa,
sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.
28“Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba;
za su neme ni amma ba za su same ni ba.
29Da yake sun ƙi sani
ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
30da yake ba su karɓi shawarata ba
suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
31za su sami sakayyar abubuwan da suka yi
su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.
32Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su,
rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;
33amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya
yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

Currently Selected:

Karin Magana 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy