YouVersion Logo
Search Icon

Yowel 1

1
1Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.
Mamayar da fāra ta yi
2Ku ji wannan, ku dattawa,
ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar.
Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku
ko a kwanakin kakanninku?
3Ku faɗa wa ’ya’yanku,
bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu,
’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.
4Abin da ɗango ya bari
fāri masu girma sun cinye;
abin da fāri masu girma suka bari,
burduduwa ta cinye;
abin da burduduwa ta bari sauran kwari#1.4 A nan ma’anar kalmomin nan huɗu na Ibraniyanci da aka yi amfani da su da yake nuna fāra ba a san tabbatacciyar ma’anar ba. sun cinye.
5Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!
Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;
ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,
gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.
6Wata al’umma ta mamaye ƙasata,
tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;
tana da haƙoran zaki,
da zagar zakanya.
7Ta mayar da kuringar inabina kango
ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena.
Ta ɓamɓare bayansu duka
ta kuma jefar da su
ta bar rassansu fari fat.
8Ku yi makoki kamar budurwa#1.8 Ko kuwa yarinya
a cikin tsummoki
tana baƙin ciki domin mijinta#1.8 Ko kuwa wanda suka yi alkawarin aure na ƙuruciyarta.
9Hadayun hatsi da hadayun sha
an yanke su daga gidan Ubangiji.
Firistoci suna makoki,
su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.
10Filaye sun zama marasa amfani,
ƙasa ta bushe;#1.10 Ko kuwa ƙasa tana makoki
an lalatar da hatsi,
sabon ruwan inabin ya bushe,
mai kuma ba amfani.
11Ku fid da zuciya, ku manoma,
ku yi ihu, ku masu noma inabi;
ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,
saboda an lalata girbin filaye.
12Kuringar inabin ta bushe
itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,
’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,
dukan itatuwan filaye, sun bushe.
Tabbatacce farin cikin ’yan adam
ya bushe.
Kira don makoki
13Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki;
ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade.
Zo, ku kwana saye da tsummoki,
ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima,
gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha
daga gidan Allahnku.
14Ku yi shelar azumi mai tsarki;
ku kira tsarkakan taro.
Ku kira dattawa
da kuma dukan mazaunan ƙasar
zuwa gidan Ubangiji Allahnku,
ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
15Kaito saboda wannan rana!
Gama ranar Ubangiji ta kusa,
za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.#1.15 Da Ibraniyanci Shaddai
16Ba a yanke abinci
a idanunmu,
farin ciki da kuma murna
daga gidan Allahnmu ba?
17Iri suna ta yanƙwanewa
a busasshiyar ƙasa#1.17 ma’anar wannan kalma da Ibraniyanci ba ta da tabbas.
Ɗakunan ajiya sun lalace,
an rurrushe rumbunan hatsin,
gama hatsi ya ƙare.
18Ji yadda dabbobi suke nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
saboda ba su da ciyawa,
har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
19A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,
gama wuta ta cinye wurin kiwo
harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
20Har ma namun jeji suna haki gare ka;
rafuffuka sun bushe
wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.

Currently Selected:

Yowel 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy