YouVersion Logo
Search Icon

Hosiya 1

1
1Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash#1.1 Da Ibraniyanci Yowash, wani suna na Yehowash sarkin Isra’ila.
Matar Hosiya da ’ya’yanta
2Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” 3Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.
4Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila. 5A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.”
6Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama,#1.6 Lo-Ruhama yana nufin ba tausayi. gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu. 7Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji Allahnsu.”
8Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji. 9Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi,#1.9 Lo-Ammi yana nufin ba mutanena ba. gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
10“Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’ 11Mutanen Yahuda da mutanen Isra’ila za su sāke haɗu su zama ɗaya, za su kuma naɗa shugaba guda su kuma fita daga ƙasar, gama ranar za tă zama mai girma wa Yezireyel.

Currently Selected:

Hosiya 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy