YouVersion Logo
Search Icon

Mai Hadishi 1

1
Kome ba shi da amfani
1Kalmomin Malami,#1.1 Ko kuwa shugaban taro; haka ma a ayoyi 2 da kuma 12. ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.
2“Ba amfani! Ba amfani!”
In ji Malami.
“Gaba ɗaya ba amfani!
Kome ba shi da amfani!”
3Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar
da yake fama a duniya?
4Zamanai sukan zo zamanai su wuce,
amma duniya tana nan har abada.
5Rana takan fito rana ta kuma fāɗi,
ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
6Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa;
tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
7Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku,
duk da haka teku ba ya cika.
Daga inda rafuffukan suke fitowa,
a can suke komawa kuma.
8Dukan abubuwa suna kawo gajiya,
gaban magana.
Ido ba ya gaji da gani,
haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
9Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance,
abin da aka yi za a sāke yi kuma;
babu wani abu sabo a duniya.
10Akwai wani abin da za a ce,
“Duba! Ga wani abu sabo”?
Abin yana nan, tun dā can,
ya kasance kafin lokacinmu.
11Ba a tunawa da mutanen dā,
haka su ma da ba a haifa ba tukuna
waɗanda za su biyo bayansu
ba za a tuna da su ba.
Hikima ba ta da amfani
12Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima. 13Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane! 14Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.
15Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba;
ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” 17Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
18Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.

Currently Selected:

Mai Hadishi 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy