YouVersion Logo
Search Icon

Amos 1

1
1Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.
2Ya ce,
Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona
ya kuma yi tsawa daga Urushalima;
wuraren kiwo duk sun bushe,
dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”
Hukunci a kan maƙwabtan Isra’ila
3Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Damaskus,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Domin sun ci zalunci Gileyad
zalunci mai tsanani,
4zan sa wuta a gidan Hazayel,
da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.
5Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus;
zan hallaka sarkin da yake cikin#1.5 Ko kuwa mazaunan Kwarin Awen#1.5 Awen yana nufin mugunta.
da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden.
Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,”
in ji Ubangiji.
6Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Gaza,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya
sun sayar wa Edom,
7Zan aika da wuta a katangar Gaza
ta ƙone duk kagarunta.
8Zan hallaka sarkin#1.8 Ko kuwa mazaunan Ashdod
da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon.
Zan hukunta Ekron,
har sai dukan Filistiyawa sun mutu,”
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Taya,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom,
ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,
10zan aika da wuta a Taya,
da za tă ƙone kagarunta.”
11Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Edom,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.
Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi,
babu tausayi,
domin ya ci gaba da fusata
bai yarda yă huce daga fushinsa ba.
12Zan aika wuta a Teman
da za tă ƙone kagarun Bozra.”
13Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Ammon,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.
Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu
don kawai yă ƙwace ƙasar.
14Zan sa wuta a katangar Rabba
da za tă ƙone kagarunta
za a yi kururuwa a ranar yaƙi,
faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.
15Sarkinta#1.15 Ko kuwa Molek; Ibraniyawa malkam zai je bauta,
shi da ma’aikatansa,”
in ji Ubangiji.

Currently Selected:

Amos 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy