YouVersion Logo
Search Icon

1 Tessalonikawa 1

1
1Bulus, Sila#1.1 Da Girik Silbanus, wani suna na Sila da Timoti,
Zuwa ga ikkilisiyar Tessalonikawa ta Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi.
Alheri da salama su kasance tare da ku.#1.1 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi
Godiya saboda bangaskiyar Tessalonikawa
2Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.
4Gama mun sani, ’yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, cewa ya zaɓe ku, 5domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku. 6Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar. 7Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya. 8Saƙon Ubangiji ya fito daga gare ku ne ba a Makidoniya da Akayya kaɗai ba bangaskiyarku ga Allah ta zama sananne ko’ina. Saboda haka ba ma bukata mu faɗa wani abu a kai, 9gama su kansu su suke ba da labari irin karɓar da kuka yi mana. Suna faɗin yadda kuka juyo ga Allah daga gumaka don ku bauta wa Allah rayayye da kuma na gaskiya, 10ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.

Currently Selected:

1 Tessalonikawa 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy