YouVersion Logo
Search Icon

1 Tarihi 1

1
Rubutaccen tarihi daga Adamu zuwa Ibrahim
Zuwa ’Ya’yan Nuhu Maza
(Farawa 5.1-32; 10.1-32; 11.10-32)
1Adamu, Set, Enosh,
2Kenan, Mahalalel, Yared,
3Enok, Metusela, Lamek, Nuhu.
4’Ya’yan Nuhu maza su ne,#1.4 Seftuwajin; Ibraniyanci ba su da ’Ya’yan Nuhu maza. Shem, Ham da Yafet.
Mutanen Yafet
5’Ya’yan#1.5 ’Ya’ya suna iya nufin zuriya Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 6-10, 17 da 20. Yafet maza su ne,
Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.
6’Ya’yan Gomer maza su ne,
Ashkenaz, Rifat#1.6 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da na Bulget (dubi kuma Seftuwajin da Far 10.3); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Difat da Togarma.
7’Ya’yan Yaban maza su ne,
Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
Mutanen Ham
8’Ya’yan Ham maza su ne,
Kush, Masar#1.8 Wato, Masar; haka ma a aya ta 11. Fut da Kan’ana.
9’Ya’yan Kush maza su ne,
Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.
’Ya’yan Ra’ama maza su ne,
Sheba da Dedan
10Kush shi ne mahaifin#1.10 Mahaifi na iya nufin kaka ko wanda ya riga Ko kuwa wanda yake tushe; haka ma a ayoyi 11, 13, 18 da 20.
Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.
11Masar shi ne mahaifin
Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa, 12Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.
13Kan’ana shi ne mahaifin
Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa, 14Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa 15Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, 16Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.
Semiyawa
17’Ya’yan Shem maza su ne,
Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
’Ya’yan Aram maza su ne,
Uz, Hul, Geter da Meshek.
18Arfakshad shi ne mahaifin Shela,
Shela kuwa shi ne mahaifin Eber.
19Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.
Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan.
20Yoktan shi ne mahaifin
Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera 21Hadoram, Uzal, Dikla, 22Ebal, Abimayel, Sheba, 23Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
Zuriyar Shem
(Farawa 11.10-26)
24Shem, Arfakshad,#1.24 Da Ibraniyanci; waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin suna da Arfakshad, Kainan (dubi kuma sharhi a Far 11.10). Shela,
25Eber, Feleg, Reyu
26Serug, Nahor, Tera
27da Abram (wato, Ibrahim).
Iyalin Ibrahim
(Farawa 25.1-4,12-16)
28’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.
Zuriyar Hagar
29Waɗannan su ne zuriyarsu.
Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, 30Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema 31Yetur, Nafish da Kedema.
Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza.
Zuriyar Ketura
32’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne,
Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
’Ya’yan Yokshan maza su ne,
Sheba da Dedan.
33’Ya’yan Midiyan maza su ne,
Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a.
Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.
Zuriyar Saratu
34Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku.
’Ya’yan Ishaku maza su ne,
Isuwa da Isra’ila.
’Ya’yan Isuwa maza
(Farawa 36.1-14)
35’Ya’yan Isuwa maza, su ne,
Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora
36’Ya’yan Elifaz maza su ne,
Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz,
da Timna wanda aka haifa wa Amalek.#1.36 Waɗansu rubuce-rubucen hannun Seftuwajin (dubi Far 36.12); Ibraniyanci yana da Gatam, Kenaz, Timna da Amalek
37’Ya’yan maza Reyuwel su ne,
Nahat, Zera, Shamma da Mizza.
Mutanen Seyir a Edom
(Farawa 36.20-43)
38’Ya’yan Seyir maza su ne,
Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.
39’Ya’yan Lotan maza su ne,
Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.
40’Ya’yan Shobal maza su ne,
Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
’Ya’yan Zibeyon maza su ne,
Aiya da Ana.
41Ɗan Ana shi ne,
Dishon.
’Ya’yan Dishon maza su ne,
Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
42’Ya’yan Ezer maza su ne,
Bilhan, Za’aban da Ya’akan.
’Ya’yan Dishan maza su ne,
Uz da Aran.
Masu mulkin Edom
43Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta.
Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.
44Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.
45Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.
46Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.
47Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.
48Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.
49Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.
50Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab. 51Hadad shi ma ya mutu.
Manyan Edom su ne,
Timna, Alwa, Yetet 52Oholibama, Ela, Finon 53Kenaz, Teman, Mibzar, 54Magdiyel da Iram.
Waɗannan su ne manyan Edom.

Currently Selected:

1 Tarihi 1: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy