1
Far 9:12-13
Littafi Mai Tsarki
HAU
Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa, na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya.
Compara
Explorar Far 9:12-13
2
Far 9:16
Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da suke bisa duniya.”
Explorar Far 9:16
3
Far 9:6
“Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.
Explorar Far 9:6
4
Far 9:1
Allah kuwa ya sa wa Nuhu da 'ya'yansa albarka, ya ce musu, “Ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku cika duniya.
Explorar Far 9:1
5
Far 9:3
Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.
Explorar Far 9:3
6
Far 9:2
Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku.
Explorar Far 9:2
7
Far 9:7
Amma ku, ku yi 'ya'ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”
Explorar Far 9:7