L.Fir 4

4
Hadayu domin Zunubi
(L.Fir 6.25-30)
1Ubangiji ya kuma ce wa Musa, 2ya faɗa wa mutanen Isra'ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka'idodin nan.
3Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama'a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata. 4Zai kawo ɗan bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, ya ɗibiya hannunsa a kan kan bijimin, ya yanka shi a gaban Ubangiji. 5Shi kuma keɓaɓɓen firist ɗin ya ɗibi jinin bijimin ya kai shi a alfarwa ta sujada. 6Ya tsoma yatsansa cikin jinin, ya yayyafa jinin sau bakwai a gaban Ubangiji a wajen labulen Wuri Mai Tsarki. 7Zai kuma ɗiba daga cikin jinin, ya sa a bisa zankayen bagaden ƙona turaren da suke cikin alfarwar a gaban Ubangiji. Sauran jinin bijimin kuwa zai zuba shi a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada. 8Zai ɗebe dukan kitsen ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi, da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa, 9da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama. 10Zai cire su daidai kamar yadda akan cire na bijimin hadaya ta salama. Sai firist ɗin ya ƙone su a kan bagaden ƙona hadaya. 11Amma fatar ɗan bijimin, da namansa, da kansa, da ƙafafunsa, da kayan cikinsa, da tarosonsa, 12da sauran bijimin duka zai kai su waje bayan zango a wuri mai tsabta inda ake zubar da toka, nan zai ƙone su da wuta a inda ake zubar da tokar.
13Idan taron jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi. 14Amma sa'ad da zunubin da suka aikata ya sanu, taron jama'a za su ba da ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi. Za a kawo shi a gaban alfarwa ta sujada. 15Sai dattawan jama'a su ɗibiya hannunsu a kan kan bijimin a gaban Ubangiji, sa'an nan a yanka bijimin a gaban Ubangiji. 16Sai keɓaɓɓen firist ya ɗibi jinin bijimin, ya kai cikin alfarwa ta sujada. 17Sa'an nan ya tsoma yatsansa a cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen. 18Sai ya ɗiba daga cikin jinin ya shafa wa zankayen bagaden da suke cikin alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, sauran jinin kuwa sai ya zuba a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada. 19Zai kwashe kitsensa duka, ya ƙone shi bisa bagaden. 20Sai ya yi da ɗan bijimin kamar yadda ya yi da ɗan bijimi na hadaya don zunubin firist. Ta haka firist zai yi kafara domin jama'a, za a kuwa gafarta musu. 21Zai kai bijimin a bayan zango, ya ƙone shi kamar yadda ya yi da na farin, gama hadaya ce don zunubin taron jama'ar.
22Idan shugaba ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. 23Idan aka sanar da shi zunubin da ya yi, sai ya kawo bunsuru marar lahani don yin hadaya. 24Zai ɗibiya hannunsa a kan kan bunsurun, ya yanka a wurin da ake yanka hadaya ta ƙonawa a gaban Ubangiji, gama hadaya ce don zunubi. 25Sai firist ya ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden. 26Firist ɗin zai ƙona kitsen duka a bisa bagaden kamar yadda akan yi da kitsen hadaya ta salama, ta haka firist zai yi kafara domin zunubin shugaban, za a kuwa gafarta masa.
27 # L.Ƙid 15.27,28 In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi. 28Sa'ad da aka sanar da shi zunubin da ya aikata, sai ya kawo akuya marar lahani don yin hadaya saboda zunubinsa. 29Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa. 30Firist zai ɗibi jinin da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden. 31Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
32Idan kuwa daga cikin 'yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo 'yar tunkiya marar lahani. 33Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa. 34Sai firist ya ɗibi jinin abin yin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sauran jinin kuwa ya zuba a gindin bagaden. 35Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi masa kafara saboda zunubin da ya aikata, za a kuwa gafarta masa.

目前选定:

L.Fir 4: HAU

高亮显示

分享

复制

None

想要在所有设备上保存你的高亮显示吗? 注册或登录