Eze 39
39
Cin Nasara a kan Gog
1“Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa Gog shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal cewa, ‘Ni Ubangiji Allah ina gāba da kai. 2Zan juya ka in sa ka gaba in tashi daga ƙurewar arewa, in kawo ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra'ila. 3Sa'an nan zan karya bakan da yake a hannun hagunka, in sa kiban da suke a hannun damanka su fāɗi. 4Za ka fāɗi matacce a kan duwatsun Isra'ila, kai da dukan rundunanka, da jama'ar da suke tare da kai. Zan ba da gawawwakinka ga tsuntsaye da dabbobi masu cin nama. 5Za ka mutu a filin saura, gama haka ni Ubangiji Allah na faɗa.’ 6Zan aika da wuta a kan Magog, da a kan waɗanda suke zaman lafiya a ƙasashen gāɓar teku, za su kuwa sani ni ne Ubangiji. 7Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama'ata, wato Isra'ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra'ila.
8“Ga shi, ranar da na ambata tana zuwa, hakika kuwa tana zuwa, ni Ubangiji Allah na faɗa. 9Sa'an nan su mazaunan biranen Isra'ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai. 10Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.
11“A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra'ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da take tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog. 12Jama'ar Isra'ila za su yi wata bakwai suna binne su don su tsabtace ƙasar. 13Dukan jama'ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa. 14A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko'ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta. 15Sa'ad da waɗannan suke bibiyawa a cikin ƙasar, duk wanda ya ga ƙashin mutum, sai ya kafa wata alama kusa da ƙashin don masu binnewa su gani, su ɗauka, su binne a Kwarin Rundunar Gog. 16Akwai gari a wurin, za a sa masa suna Hamona, wato runduna. Ta haka za su tsabtace ƙasar.
17 #
W.Yah 19.17,18 “Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko'ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra'ila. Za su ci nama su kuma sha jini. 18Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da 'yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan. 19Za su ci kitse, har su gundura, su sha jini kuma, har su bugu a idin da nake shirya musu. 20Za a ƙosar da su da naman dawakai, da na mahayansu da na mutane masu iko, da na dukan mayaƙa, ni Ubangiji na faɗa.”
Komowar Mutanen Isra'ila
21“Zan nuna ɗaukakata a cikin al'ummai, dukan al'ummai kuwa za su ga hukuncin da na yi da ikon da na nuna kansu. 22Tun daga wannan rana har zuwa gaba, jama'ar Isra'ila za su sani, ni ne Ubangiji Allahnsu. 23Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi. 24Na yi gwargwadon lalatarsu da laifofinsu, na kawar da fuskata daga gare su.
25“Saboda haka, ni Ubangiji Allah, na ce yanzu zan komo da zuriyar Yakubu daga bauta in nuna mata jinƙai. Zan yi kishi domin sunana mai tsarki. 26Sa'ad da suka komo suka zauna lafiya a ƙasarsu, za su manta da abin kunyar da suka yi da dukan ha'incin da suka yi mini. Ba wanda zai ƙara firgita su, ba kuwa mai tsorata su. 27Zan nuna wa sauran al'umma ni mai tsarki ne ta wurin komo da mutanen Isra'ila daga cikin al'ummai, da ƙasashen al'ummai magabtansu. 28Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu, domin na kore su daga ƙasarsu zuwa bautar talala cikin al'ummai, sa'an nan na sāke tattaro su zuwa cikin ƙasarsu. Daga cikinsu ba zan bar ko ɗaya a cikin al'ummai ba. 29Ba kuma zan ƙara kawar da fuskata daga gare su ba, sa'ad da na saukar da Ruhuna a kan jama'ar Isra'ila, ni Ubangiji na faɗa.”
Nu geselecteerd:
Eze 39: HAU
Markering
Kopiëren
Vergelijk
Delen
Wil je jouw markerkingen op al je apparaten opslaan? Meld je aan of log in
@Bible Society of Nigeria 1979