1
Yak 3:17
Littafi Mai Tsarki
HAU
Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.
Vergelijk
Ontdek Yak 3:17
2
Yak 3:13
Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali'u da hikima suke sawa.
Ontdek Yak 3:13
3
Yak 3:18
Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.
Ontdek Yak 3:18
4
Yak 3:16
A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke.
Ontdek Yak 3:16
5
Yak 3:9-10
Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah. Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!
Ontdek Yak 3:9-10
6
Yak 3:6
Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.
Ontdek Yak 3:6
7
Yak 3:8
amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa.
Ontdek Yak 3:8
8
Yak 3:1
Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani.
Ontdek Yak 3:1