Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri, muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.