Ta wurin bangaskiya Musa, sa'ad da ya girma, ya ƙi yarda a kira shi ɗan 'yar Fir'auna, ya gwammaci ya jure shan wuya tare da jama'ar Allah, da ya mori romon zunubi, mai saurin wucewa. Ya amince, cewa wulakanci saboda Almasihu wadata ce a gare shi, fiye da dukiyar ƙasar Masar, domin ya sa ido a kan sakamakon. Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa.