YouVersion Logo
Search Icon

Luk 17

17
Sanadodin Yin Zunubi
(Mat 18.6-7,21-22; Mar 9.42)
1Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu! 2Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku. 3#Mat 18.15 Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi. 4Ko ya yi maka laifi sau bakwai rana ɗaya, sa'an nan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, ‘Na tuba,’ sai ka yafe shi.”
Ƙara Mana Bangaskiya
5Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.” 6Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.”
Wajibin Bawa
7“Misali, wane ne a cikinku in yana da bawa mai yi masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, ‘Maza, zo ka zauna, ka ci abinci’? 8Ashe, ba ce masa zai yi, ‘Shirya mini jibi, ka kuma yi ɗamara, ka yi mini hidima, har in gama ci da sha, daga baya kai kuma ka ci ka sha,’ ba? 9Yā gode wa bawan nan don ya bi umarni? 10Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibinmu kurum.’ ”
Yesu Ya Warkar da Kutare Goma
11Wata rana yana tafiya Urushalima, sai ya bi iyakar ƙasar Samariya da Galili. 12Yana shiga wani ƙauye ke nan, sai waɗansu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa. 13Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu,” 14#L.Fir 14.1-32 Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka. 15Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi, 16ya fāɗi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne. 17Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran? 18Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah, sai baƙon nan kaɗai?” 19Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”
Bayyanar Mulkin Allah
(Mat 24.23-28,36-41)
20Da Farisiyawa suka tambaye shi lokacin bayyanar Mulkin Allah, ya amsa musu ya ce, “Ai, bayyanar Mulkin Allah ba ganinta ake yi da ido ba. 21Ba kuwa za a ce, ‘A! Ga shi nan,’ ko kuwa, ‘Ga shi can,’ ba. Ai, Mulkin Allah a tsakaninku yake.”
22Ya kuma ce wa almajiran, “Lokaci na zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba. 23Za su ce muku, ‘A! ga shi nan,’ ko kuwa, ‘Ga shi can!’ Kada ku je, kada ku bi su. 24Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, haka ma, Ɗan Mutum zai zama a ranar bayyanarsa. 25Amma lalle sai ya sha wuya iri iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi. 26#Far 6.5-8 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Ɗan Mutum. 27#Far 7.6-24Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka. 28#Far 18.20—19.25 Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine, 29amma a ranar da Lutu ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka. 30Haka kuma zai zama a ranar bayyanar Ɗan Mutum. 31#Mat 24.17,18; Mar 13.15,16 A ran nan fa wanda yake kan soro, kayansa kuma na cikin gida, kada ya sauko garin ɗaukarsu. Haka kuma wanda yake gona, kada ya juyo. 32#Far 19.26 Ku tuna fa da matar Lutu. 33#Mat 10.39; 16.25; Mar 8.35; Luk 9.24; Yah 12.25 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi. 34Ina gaya muku, a wannan dare za a ga mutum biyu a gado ɗaya, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 35Za a ga mata biyu suna niƙa tare, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. 36[Za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.]” 37Sai suka amsa suka ce, “Ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “A inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.”

Currently Selected:

Luk 17: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy