Eze 37:7-8

Eze 37:7-8 HAU

Sai na yi annabci kamar yadda ya umarce ni. Da na yi annabcin sai aka ji motsi da girgiza. Sai ƙasusuwan suka harhaɗu da juna, ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu. Da na duba, sai ga jijiyoyi a kansu, nama kuma ya baibaye su, sa'an nan fata ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.

Video voor Eze 37:7-8