1Bit 5:8-9
1Bit 5:8-9 HAU
Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame. Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san 'yan'uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya.









