1
Luk 6:38
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”
Vergelijk
Ontdek Luk 6:38
2
Luk 6:45
Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”
Ontdek Luk 6:45
3
Luk 6:35
Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.
Ontdek Luk 6:35
4
Luk 6:36
Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”
Ontdek Luk 6:36
5
Luk 6:37
“Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.
Ontdek Luk 6:37
6
Luk 6:27-28
“Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri. Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a.
Ontdek Luk 6:27-28
7
Luk 6:31
Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.
Ontdek Luk 6:31
8
Luk 6:29-30
Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma. Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi.
Ontdek Luk 6:29-30
9
Luk 6:43
“Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan 'ya'ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan 'ya'ya.
Ontdek Luk 6:43
10
Luk 6:44
Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.
Ontdek Luk 6:44