1
Yah 4:24
Littafi Mai Tsarki
HAU
Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
Vergelijk
Ontdek Yah 4:24
2
Yah 4:23
Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
Ontdek Yah 4:23
3
Yah 4:14
Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”
Ontdek Yah 4:14
4
Yah 4:10
Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”
Ontdek Yah 4:10
5
Yah 4:34
Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
Ontdek Yah 4:34
6
Yah 4:11
Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai?
Ontdek Yah 4:11
7
Yah 4:25-26
Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.” Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganan nan da yake.”
Ontdek Yah 4:25-26
8
Yah 4:29
“Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”
Ontdek Yah 4:29