1
Eze 33:11
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’
Vergelijk
Ontdek Eze 33:11
2
Eze 33:7
“Yanzu fa, kai ɗan mutum, na sa ka zama ɗan tsaro a al'ummar Isra'ila. Duk lokacin da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su.
Ontdek Eze 33:7
3
Eze 33:9
Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.”
Ontdek Eze 33:9
4
Eze 33:6
Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.’
Ontdek Eze 33:6
5
Eze 33:5
Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa.
Ontdek Eze 33:5