1
Afi 6:12
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.
Vergelijk
Ontdek Afi 6:12
2
Afi 6:18
a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.
Ontdek Afi 6:18
3
Afi 6:11
Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis.
Ontdek Afi 6:11
4
Afi 6:13
Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.
Ontdek Afi 6:13
5
Afi 6:16-17
Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita. Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah
Ontdek Afi 6:16-17
6
Afi 6:14-15
Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku, shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.
Ontdek Afi 6:14-15
7
Afi 6:10
A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.
Ontdek Afi 6:10
8
Afi 6:2-3
Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don al'amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
Ontdek Afi 6:2-3
9
Afi 6:1
Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.
Ontdek Afi 6:1